Kayayakin agajin jin kai da dama sun isa Zirin Gaza.

A wata sanarwar da babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ayyukan jin kai a Gaza Tom Fletcher, tun bayan da yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki makwanni biyu da suka gabata, motocin dauke da rumfuna, abinci da magunguna har ma da ruwan sha ne suka isa Gaza.

Jami'in na Majalisar Dinkin Duniya ya mika godiyarsa ga duk wadanda suka taimaka wajen cimma wannan mataki na kai dauki ga Falasdinawa a wannan lokaci da suke da matukar bukata.

Jawabin nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirye-shiryen shiga mataki na biyu na yarjejeniyar wadda ake fatan ta kawo karshen yakin gabaki dayansa.

To sai dai bayanan shugaba Amurka Donald Trump na karbe Gaza na saka shakku a kan makomar yarjejeniyar.

 

Karin Bayani: Martani kan barazanar Trump na kwace iko da Gaza  


News Source:   DW (dw.com)