Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya bukaci hadin kan al'ummar sa a daidai lokacin da rayuwa a kasar ke kara tsada, musamman ma hauhawar da farashin kayayakin masarufi ke yi.
Mahukuntan na Berlin sun yi wannan kira ga Jamusawa ne a yayin da suke kokarin kafa kwamiti da ya hada da masana tattalin arziki da yan kasuwa da shugabannin manyan bakunan kasar domin lalubo mafita ga wannan matsalar.
Da yake magana da kamfanin dillancin labarai na DPA, shugaban cibiyar binciken fannin tattalin arziki da ke kasar Marcel Fratzscher ya ce halin da al'umma suka shiga a yanzu haka, karin albashi da kuma tallafi daga gwamnati ne kawai zai fidda su.
A ranar Litinin da ke tafe ne za a fara wannan zama na musamman da ke da nufin kawo karshen matsalar rayuwa da ta samo asali daga rikicin kasashen Rasha da Ukraine.