A ranar Alhamis Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ta karbi kason farko na alluran rigakafin cutar kyandar biri.
Hukumomin lafiya na ganin alluran za su taimaka wajen rage yaduwar cutar da ta tilasta wa Majalisar Dinkin Duniya ayyanata a matsayin barazana ga lafiya.
Najeriya za ta fara rigakafin kyandar biri cikin Oktoba
Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ta kasance kasar da annobar ta fi kamari kuma ta yadu zuwa kasashe makwabta da kuma sauran sassan duniya.
Rashin alluran rigakafin a kasar ya haifar da tsaiko wajen dakile yaduwar cutar a tsakanin al'umma.
Kyandar biri: AU ta ce annobar na karuwa a Afrika
Kasar ta kasance wacce cutar ta fi dagula wa lissafi sakamakon jinkirin da aka samu na isan alluran.