Shugabannin kasashen Larabawa sun yi ganawar ce kan shirin sake gina Zirin Gaza, a wani mataki na taka birki ga kudurin Shugaba Donald Trump na Amurka na mallakar Zirin tare da rarraba mazauna Gazan zuwa wasu kasashen.
Wata majiya daga gwamnatin Saudiyya ta tabbatar da cewa, shugabanin sun tashi taron ba tare sun wallafa sanarwar karshen taro ba. To sai dai a ganawarsa da Shugaba Trump a ranar 11 ga watan Fabarairu, Sarkin Jordan Abdullahi II, ya ce Masar za ta gabatar da shiri da zai kai su ga mataki na gaba.
Karin bayani: Kasashen Larabawa na adawa da kwace Gaza
Dukannin kasashen Larabawan sun yi fatali da kudurin Shugaba Trump, sai dai akwai rarrabuwar kawuna kan wanda ya kamata ya shugabanci Gaza da kuma yadda za a tattara kudin sake gina ta. Yakin da aka kwashe fiye da watannin 15 ana gabza yaki tsakanin Isra'ila da Hamas ya daidaita Zirin, inda Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa, ana bukatar fiye da dala biliyan 53 domin sake gina Zirin.