Kasashen Larabawa na adawa da kwace Gaza

Kamfanin dillancin labaran kasar ta Hadaddiyar Daular Larabawa WAM ne ya ruwaito hakan, inda ya ce kalaman na Shugaba Sheikh Mohammed bin Zayed na zuwa ne sakamakon kudurin shugaban Amurka Donald Trump na kwace iko da yankin Zirin Gaza na Falasdinu tare da raba mazauna yankin zuwa kasashe makwabta.

Gaza: Cimma yarjejeniyar tsagaita wuta

To view this video please enable JavaScript, and consider upgrading to a web browser that supports HTML5 video

02:06

Al Nahyan ya bayyanawa sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio da ke ziyara a yanzu haka a birnin  Abu Dhabi bayan kai ziyara a Isra'ila da Saudiyya cewa, yana da muhimmanci a alakanta gyaran yankin na Zirin Gaza da matakin kawo karshen rikicin Isra'ila da Falasdinu na din-din-din ta hanyar samar da kasashe biyu.

Falasdinawa a Gaza na cikin mawuyacin hali

Adadin wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata a Gaza na karuwa yayin da Isra'ila ke ci gaba da daukar fansa na hare-haren ta'addancin Hamas.

Hoto: Fatima Shbair/AP/picture alliance Gazastreifen | Trauer um Verstorbene nach israelischen Vergeltungs Luftangriffen

Isra'ila ta tsananta hare-haren ramuwar gayya a Gaza

Isra'ila ta tsananta kai hare-hare ta sama a zirin Gaza kwanaki bayan da Hamas ta kaddamar da hare-hare. Kungiyar EU da Amurka da sauran kasashe sun ayyana Hamas mai iko da Gaza a matsayin kungiyar ta'addanci. Firayiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce "abin da za mu yi wa makiyanmu a cikin kwanaki masu zuwa za a jima ba a manta ba."

Hoto: Belal Al SabbaghAFP/Getty ImagesDestroyed residential blocks in Gaza after Israel’s retaliatory strikes

An lalata gine-gine masu yawa

Daruruwan gine-gine ne suka lalace gaba daya, daura da wasu dubbai da suka lalace sosai sakamakon hare-haren Isra'ila, a cewar ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya (OCHA). Dubban mutane ne aka ce ba su da ruwa.

Hoto: Mohammed Talatene/dpa/picture allianceSmokes rises following an Israeli air strike on Gaza City

Neman wadanda suka makale

Masu aikin ceto na neman wadanda suka tsira bayan harin da Isra'ila ta kai kan sansanin 'yan gudun hijira na Jabalia da ke arewacin Gaza. Ya zuwa yanzu, sama da mutane 1,000 suka mutu yayin da wasu fiye da 5,000 suka jikkata bayan hare-haren jiragen sama a yankin da ke karkashin ikon Hamas, a cewar hukumomin yankin.

Hoto: Mahmud Hams/AFP/Getty ImagesRescue workers search for survivors after Israeli airstrikes hit Jabaliya refugee camp in north of Gaza

Makokin wadanda suka mutu

Wata mata ta yi kuka yayin da aka dora gawarwaki a kan babbar mota, bayan wani harin da Isra'ila ta kai. A cewar hukumar lafiya ta Gaza, an kashe fiye da yara 200 da mata sama da 100 a Gaza.

Hoto: Said Khatib/AFP/Getty ImagesA woman wails as she raises her hands, as men load blanketed bodies onto a truck in the background

An rufe Gaza

Falasdinawa na tserewa harin Isra'ila. A cewar Majalisar Dinkin Duniya, fiye da mutane 187,000 ne a Gaza suka rasa matsugunansu, kana sama da dubu 100 suka yi mafaka a makarantun MDD, yayin da wasu 40,000 suka kaurace wa gidajensu. Shi kansa ficewa daga zirin Gaza abu ne mai wuya kasancewar Isra'ila ta rufe yankin tare da rufe mashigar Masar.

Hoto: Saleh Salem/REUTERSSeveral people in Gaza are seen sitting on a bus with all their belongings

Sojojin Isra'ila suna iko da iyakar Gaza

Ana ganin sojojin Isra'ila suna sintiri a kan iyakar Isra'ila da Gaza. Mayakan Hamas sun kutsa shingen kan iyaka a wurare da dama a cikin daren ranar 7 ga watan Oktoba kafin su kai hare-hare a yankin Isra'ila. Isra'ila ta gina shinge kan iyakar Gaza a shekara ta 1994. An kuma rufe kan iyakar Gaza da Masar da dogon shinge.

Hoto: Oren Ziv/AP/picture allianceIsraeli troops are seen patrolling the Israel-Gaza border

Sojojin Isra'ila su na kan iyakar Gaza

Bayan da Isra'ila ta fitar da karin sojoji 300,000, mazauna Gaza da dama na fargabar cewa, akwai yiwuwar kaddamar da harin Isra'ila ta kasa. Motocin soji da kayan yaki sun cika kan iyakar Gaza. An kwashe kusan dukkan mautanen da ke garuruwan Isra'ila da ke kan iyaka da Gaza gaba daya.

Hoto: Ilia Yefimovich/dpa/picture allianceIsraeli forces patrol areas along the Israeli-Gaza border

Mummunan yanayi na bukatar jinkai

Da yake magana da CNN, Jan Egeland, babban sakataren hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Norway, ya yi gargadin tagaiyarar al'umma a Gaza. "Zai kai ga aikata laifukan yaki idan yara za su mutu da yunwa a asibitoci saboda rashin wutar lantarki misali,"

Hoto: Mahmud Hams/AFP/Getty ImagesPalestinians salvage household items from damaged apartments following Israeli airstrikes

Shugaban Hamas a Gaza, Yahya Sinwar

Yahya Sinwar ya kasance shugaban kungiyar Hamas a Gaza tun a shekarar 2017. Ana masa kallon daya daga cikin wadanda suka shirya harin ta'addancin da aka kai kan Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba. An ambato Sinwar, wanda ya taso a sansanin 'yan gudun hijira na Gaza yana cewa, "gwamma mu mutu a matsayin shahidai da mu mutu saboda zalunci da wulakanci."

Hoto: Mohammed Abed/AFPHamas Gaza leader Yahya Sinwar

Tsanantar tashe-tashen hankula

Wani mai magana da yawun Hamas ya shaida wa manema labarai cewa, a duk lokacin da Isra'ila ta kai hari a kan fararen hula a Gaza ba tare da yin gargadi ba, to za a kashe daya daga cikin 'yan Isra'ila da ake garkuwa da su. Ministan harkokin wajen Isra'ila Eli Cohen ya yi gargadin cewa babu yafiya kan irin wannan mataki.

Hoto: Mahmud Hams/AFP/Getty ImagesA fireball erupts from an Israeli airstrike in Gaza City Hotuna 101 | 10Hotuna 10

Matakin na Hadaddiyar Daular Larabawa kan wannan rikici na da matukar muhimmanci, kasancewarta guda cikin Kasashen Larabawa hudu da suka kulla kawance da Isra'ila a lokacin mulkin Trump na farko da kuma yadda ta taka rawa wajen sake gina Gazan a lokutan baya.

 


News Source:   DW (dw.com)