Kasashen AES za su kaddamar da sabon fasfo na bai daya

Kasashen Mali da Nijar da Burkina Faso za su fara aiki da sabon fasfo na bai daya daga ranar 29 ga wannan watan na Janairu, ranar da wa'adin da suka dauka na raba gari da kungiyar ECOWAS ke cika kamar yadda shugaban kungiyar da suka kafa ta AES ya sanar a Alhamis din nan.

Sai dai sanarwar ta janar Assimi Goita da ke shugabancin kungiyar ta ce duk da haka masu tsohon fasfo na ECOWAS za su iya ci gaba da amfani da shi har i zuwa lokacin da zai kare aiki, amma daga wannan lokaci za su iya canja shi da sabon da aka fitar mai dauke da tambarin AES.

Gwamnatocin kasashen uku da ke karkashin mulkin sojoji sun yanke shawarar ballewa daga ECOWAS saboda zarginta da zama 'yar amshin shatan Faransa wadda ta yi musu mulkin mallaka amma suka juya mata baya.

Karin bayani: Shugaban Senegal zai sasanta ECOWAS da AES

Kaddamar da wannan sabon fasfo na nufin kasashen na AES sun yi nisa ba sa jin kira kan matakin da suka dauka, duk kuwa da nadin shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye a matsayin mai shiga tsakani domin sauya musu tunanin don dawowa cikin dangi.


News Source:   DW (dw.com)