Kasashe sun gaza cika kudirin kare muhalli

Kusan dukkan kasashen duniya ciki har da manyan kasashe masu ci gaban masana'antu sun gaza cika kudirorinsu na gabatar da sabbin matakan yaki da sauyin yanayi a yayin da wa'adin da Majalisar Dinkin Duniya ta bayar yake cika a wannan Litinin.

Kasashe goma ne kacal daga cikin kasashe kimanin 200 da suka rattaba hannu kan yaarjejeniyar sauyin yanayi na birnin Paris suka mika jadawalin shirin su na muhallin kafin cikar wa'adin na ranar 10 ga watan Fabrairu kamar yadda alkaluman Majalisar Dinkin Duniyar suka nunar.

A karkashin yarjejeniyar, ya kamata kowace kasa ta gabatar da cikakken tsarin jadawali na rage hayakin masan'antu nan da shekarar 2035 da kuma yadda za su aiwatar da shi.

Galibin kasashen kungiyar G20 masu ci gaban masana'antu ciki har da Amurka da Burtaniya da Brazil wadda ke karbar bakuncin taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayin na bana basu iya cika alkawuransu ba.

 


News Source:   DW (dw.com)