Kasashe mambobin kungiyar Tarayyar Turai sun cimma yarjejeniya don sabunta takunkumin da aka sanya wa Rasha tun bayan da ta mame kasar Ukraine. Cikin wani sako da ta wallafa a kafar X, shugabar diflomasiyyar EU, Kaja Kalas, ta ce kasar Hangari ta sauko daga kujerar na ki da ta hau kan sabunta takunkumai ga Rasha a yayin taron ministocin harkokin waje da ke gudana a Brussels.
Karin bayani: Putin babban aminin Turai ya zama makiyinta
Tuni dai Tarayyar Turai ta kakaba wa Rasha takunkumai 15 tun bayan mamayar da ta yi wa Ukraine a ranar 24 ga watan Fabrairun 2022. Dama dai, dole ne duk membobin EU su goyi bayan irin wannan shawarar aza takunkumai kafin a amince da ita a hukumance, ko kuma su daina aiki ne a ranar 31 ga watan Janairun 20224.
Karin bayani: Yakin Ukraine na kara yin muni
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ma'aikatar tsaron Rasha ta yi ikirarin kwato kauyen Nikolayev-Darinoda ke yankin Kursk da sojojin Ukraine suka kama yayin farmakin da suka kai a bazarar da ta gabata. Sai dai Ukraine ta ce har yanzu tana rike da murabba'in kilomita 100 na yankin Kursk, lamarin da ake gani a matsayin wata dabarar share fagen shiga shawarwarin zaman lafiya.