Rahoton na bankin duniya ya ce kasashen 26 suna cikin mawuyaci fiye da kowane lokaci tun shekaru 2006.
Kasashen sun hada da Afghanistan da Yemen da Koriya ta Arewa. Sauran kasashen suna yankin Afirka ne kudu da hamadar Sahara sun kuma hada da Habasha da Chadi.
A cewar Bankin duniyar kasashen sun fi fadawa talauci a yanzu fiye da yadda suke a lokacin annobar korona duk da cewa sauran kasashen duniya tattalin arzikinsu ya farfado