Kasar Yuganda ta aike da sojoji zuwa arewa maso gabashin DR Kwango

Kakakin rundunar tsaron Yuganda Felix Kulayigye ya ce sun dauki wannan mataki na tura sojoji garin Bunia da sahalewar mahukuntan Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango don gudanar da ayyukan hadin gwiwa biyo bayan karuwar kisan gillar da 'yan bindiga ke yi wa al'umma.

Karin bayani: Ilimi ya tabarbare sakamakon rikici a gabashin Kwango

Garin  Bunia da ke kusa da Tafkin Albert da Yuganda ya kasance gurin da ake samun hare-hare a kai a kai daga kungiyoyi masu dauke da makamai musamman ma M23 da ke da alaka da kungiyar 'yan tawayen Yuganda ta AFD.

Wannan mataki na zuwa a daidai lokacin da 'yan tawayen M23 da dakarun kawarsu Ruwanda ke ci gaba da matsa lamba a gabashin Kwango bayan kwace iko da garin Bukavu babban birnin Lardin Kivu ta Kudu.

A baya dai kwararru sun yi zargin Yuganda da tallafa wa 'yan tawayen M23 tare da ba su damar yin amfani da yankinta a matsayin hanyar shigo da makamai, zargin da fadar mulki ta Kampala ta yi watsi da shi.


News Source:   DW (dw.com)