Karuwar makaman nukiliya a duniya

Karuwar makaman nukiliya a duniya
Cibiyar nazarin zaman lafiya da ke Stockholm (SIPRI) ta ce za a samu karuwar makaman nukiliya a duniya saboda tashe tashen hankula da suka mamaye ko'ina.

Duk da cewar an samu raguwar adadin jimillar makaman nukiliya zuwa kimanin 12,705 a fadin duniya, a rahotanta na shekara shekara da aka wallafa a wannan Litinin, cibiyar binciken zaman lafiya ta ce tabbas wannan adadin zai karu cikin shekaru goma masu zuwa.

Kwararre a cibiyar Hans Kristensen ya bayyana cewar, alamun raguwar makaman nukiliya tun bayan da aka kawo karshen yakin cacar baka ya zo karshe, kuma idan kasashen da ke mallakar makaman nukiya basu dauki matakai ba, akwai yiwuwar habakarsu fiye da yadda ake a yanzu.

Rahoton na SIPRI na nuni da cewar har yanzu Rasha Amurka ne ke mallakar kaso 90 na makaman nukiliyar da duniya ke da su, inda Moscow ke mallakar 5,977 kana Washinton 5,428.

 


News Source:   DW (dw.com)