Jami'in da ke goyon bayan Rasha ya ce ba a sami wata barna ba. Gwamnan Sevastopol ya ce jiragen saman Rasha na yaki sun harbo wani jirgin mara matuki na Ukraine.
Ko da yake babu wani tabbaci kan sahihancin faya-fayan bidiyon, sashin tattara labarai na Ukraine ya wallafa faya-fayan da suka nuna yadda aka harba roka a sararin samaniya da kuma karar ababen fashewa biyu. Ko a makon da ya gabata, an sami fashewar abubuwa a sansanin sojin sama na Crimea.