Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira ga Rasha da ta mutunta makamashin wutar lantarkin da Ukraine ta ke samu daga tashar makamashi ta Zaporijjia, wadda yanzu hakan ta karbe iko da ita.
Mista Guterres ya ce ganin cewar wutar lantarki da tashar makamashin ke bayarwa ta Ukraine ce, a don haka ya zama wajibi da Rasha ta mutuntata batun ba tare da wata fargaba ba.
Antonio Guterres na kalamun ne a yayin da yake ziyara a gabar teku ta Odessa a wannan Jumma'ar, inda ake jigilar kayan abinci daga Ukraine zuwa wasu kasashen duniya.
Masana dai na hasashen ko Rasha ka iya katse tashar makamashin mafi girma a nahiyar Turai, tun bayan da ta karbe iko da ita tamkar yadda ta yi wa takwararta ta Energoatom a baya.
Rasha da Ukraine dai na cigaba dda nuna wa juna 'yar yatsa tun bayan tashin wasu ababen fashewa a wani bangare na tashar makamashin a baya.