kanfanin Japan Airlines ya fuskanci kutse ta yanar gizo

Kamfanin jiragen saman Japan Airlines ya bayyana cewar ya fuskanci harin yanar gizo, lamarin da ya haifar da tsaiko ko soke zirga-zirgar jiragen sama. Mai magana da yawun kamfanin jirgin da ke zama na biyu mafi girma na Japan ya shaida wa kanfanin dillancin labarai na AFP cewar sun dakatar da sayar da tikiti na tsawon wannan rana ta Alhamis (26.12.2024), kuma suna kokarin shawo kan matsalolin da kutsen ya haifar.

A halin yanzu dai, akalla jiragen cikin gida guda tara da kuma na kasa da kasa da dama sun riga sun fuskanci tsaiko, kamar yadda kafafen yada labarai na cikin gidan Japan suka ruwaito. Sannan Japan Airlines ta yi hasarar darajar hannun jarin na kashi 2.5 da safiyar wannan Alhamis a kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Tokyo kafin ta murmure kadan.

Manyan kanfofin kasar Japan da dama sun fuskanci hari ta yanar gizo an watanni baya-bayannan ciki har da tashar jiragen ruwa na Nagoya da ke tsakiyar kasar da babban kamfanin kera motoci na Toyota.

 


News Source:   DW (dw.com)