Kamfanin hakar ma'adanan karkashin kasa na kasar Faransa Orano ya tabbatar da cewa Jamhuriyar Nijar ta kwace iko da bangaren kamfanin na hakar uranium da ke kasar, a wani mataki na ci gaba da yanke duk wata alaka da Faransa tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a cikin watan Yulin bara.
Karin bayani:Nijar ta kori kamfanin Orano na Faransa
Sanarwar da kamfanin ya fitar bayan taro na musamman da hukumar gudanarwarsa ta yi, ta ce yanzu dai ta tabbata ikon mahakar uranium din Orano da ke Somair ya koma hannun muhukuntan mulkin sojin Nijar, duk kuwa da gargadin da kamfanin ya jima yana yi na tsawon watanni kan batun.
Karin bayani:Gwamnatin Nijar ta gargadi kamfanin ORANO
A cikin watan Yunin da ya gabata ne gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta kwace lasisin hakar uranium din Orano, yayin da shi kuma kamfanin ya sanar da dakatar da aikinsa a cikin watan Oktoban da ya gabata, sakamakon irin matsin lambar da yake fuskanta daga hannun hukumomin Nijar.
Jamhuriyar Nijar ce kasa ta 7 a duniya cikin jerin kasashe masu arzikin sinadarin uranium.