Kamfanin man fetur na Najeriya NNPC ya sanar da karin farashin man da kashi 11 cikin 100 a Litinin din nan, karo na biyu kenan da kamfanin ke kara farashin man a cikin tsawon makonni biyu, kuma kwana guda kacal da fara sayen man daga matatar Dangote.
Karin bayani:Kamfanin NNPC ne zai sayar da man matatar Dangote a Najeriya
Da wannan kari, yanzu farashin litar mai daya a Lagos zai kasance Naira 950, yayin da a jihohin Arewa maso gabashin kasar zai zama Naira 1,019, bayan da ya sari man daga matatar Dangote a kan Naira 898 ko wace lita daya.
Karin bayani:Majalisar Dokoki za ta sasanta Dangote da NNPCL
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito cewa wannan sabon karin farashin zai jefa al'ummar Najeriya cikin kangin rayuwa da suke fama da shi a yanzu haka, a daidai lokacin hauhawar farashin kayayyaki ya karu da kashi 33.4 cikin 100.