Hukumomi a Jamhuriyar Kamaru, sun kore rade-raden da ake yi dangane da halin lafiyar Shugaba Paul Biya mai shekaru 91, bayan kwashe lokaci ba tare da ya fito a bainal jama'a ba.
Jami'ai a Kamarun sun ce Shugaba Biya na cikin halin lafiya, kuma yanzu haka yana ziyara ne a nahiyar Turai.
Cikin watan jiya ne dai aka ga shugaban na Kamaru a cikin jama'a, a lokacin taron da China ta yi da shugabannin kasashen Afirka a birnin Beijing.
Sai dai tun daga wannan lokacin ba a sake ganin sa ba; hatta a lokacin babban taron majalisar Dinkin Duniya da shugabannin kasashe suka halarta a Birnin New York.
Haka ma a lokacin taron koli na shugabannin kasashen da ke amfani da harshen Faransanci da aka yi a kasar Faransa.
Galibi Shugaba Paul Biya kan ziyarci nahiyar Turai musamman domin duba lafiyarsa.