Kogin na Rhine dai na zama daya daga cikin manyan hanyoyi na safarar kayayaki daga teku zuwa wasu sassa na kasar da ma wasu kasashen duniya.
A sanarwar da ma'aikatan sufuri ruwa suka fidda a yau Litinin, akwai yiwuwar kogin ya kara janyewa kamar yadda masu hasashen yanayi suka nuna. Kuma farashin jigilar kayayyaki ta wannan hanya na iya karuwa.
A shekarar 2018 an sami makamancin wannan matsalar ta kafewar kogin na Rhine wanda ya jagoranci karancin kayayakin da kamfanoni da dama suke bukata.