
Wani kamfani mallakar Amirka da ke kai kayayyakin kiwon lafiya da magunguna ta hanyar jirage marasa matuka ya sanar da cewar ya fara tashin jiragensa a Jihar Kaduna.
Miliyoyin mutane ne dai a yankin arewacin Najeriya ke da karancin hanyoyin samun kulawa ta kiwon lafiya musamman saboda kasancewar kungiyoyin masu jihadi. A cewar kamfanin mai sunan Zipline mai kyara jirage marasa matuka, jiragen za su isar da kayayyakin kiwon lafiya da magunguna sama da 200 a fadin Jihar Kadunan,a wani mataki na gwaji kafin hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya ta amince da aiwatar da shirin a hukumance.
News Source: DW (dw.com)