Kabila ya caccaki Tshisekedi kan yakin Kongo

Tsohon shugaban kasar Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo Joseph Kabila  ya ce rashin iya mulkin magajinsa kuma shugaban kasar na yanzu Felix Tshisekedi ne ya kai ga munanar rikici a gabashin kasar.

Kabila ya yi caccakar tasa ce a wani rubutu da ya yi a wata jaridar Afirka ta Kudu da ake kira Sunday Times inda ya yi wa shugaban da ke kan karagar mulki tatas.

Kwango ta zargi MDD da sakaci wajen daukar mataki kan M23

Mista Kabila ya ce bai kamata a daura laifin abinda ke faruwa tsakanin Kinshasa da Kigali ba a kan kungiyar M23 da ke samun goyon bayan Rwanda kadai.

Ya kara cewa tun a lokacin da Tshisekedi ya karbi mulki a shekarar 2019 bayan lashe zabe, halin da ake ciki a DRC ya fara kazanta.

Shugabannin Afirka sun bukaci tsagaita wuta a DRC

Har ila yau, Kabila ya fada cewa idan ba a magance rikicin da ke aukuwa ba to za a ci gaba da fuskantar tsamin dangantaka tsakanin DRC da Rwanda.


News Source:   DW (dw.com)