Shugaban Kasar Indonesiya Joko Widodo, wanda ke jagorantar kungiyar G20, ya isa Kyiv babban birnin kasar Ukraine a matsayin wanda ya nada kansa mai shiga tsakani na neman zaman lafiya tsakanin kasashen Rasha da Ukraine.
Daga kiev shugaban na Indonesiya zai tafi Rasha don ganawa da takwaransa Vladimir Putin,domin gabatar da bukatar kawo karshen yakin don kaucewa matsalar karancin abinci a duniya.I Indonesiya za ta karbi bakuncin taron kasashe masu arzikin masana'antu G20 a Tsibirin Bali a watan Nuwamba da ke tafe.
News Source: DW (dw.com)