Shugaba mai jiran gadon mulkin kasar Ghana, John Dramani Mahama ya ce ya zaku da ganin ya samar da sabbin sauye-sauye ga tsarin tattalin arzikin kasar da ke fama da matsaloli, abin da yake ganin ya taimaka ga rashin daidaiton da ake gani a wasu kasashe makwabtan Ghana.
Cikin hirar da ya yi da tashar DW, John Mahama ya ce lallai Ghana na iya zama kan hadarin iya fuskantar juyin mulki, shigen wanda aka gani a kasashe makwabtanta, masalan Burkina Faso da Nijar da ma Mali.
Karkashin jagorancin shugaba mai ci a yanzu Nana Afuko-Addo, tsadar kayayyaki ta karu da kaso 40%, abin kuma ya tsawwala hali na rayuwa da aka kwashe shekaru ba a ga hakan ba.
Ana dai kallon jan aiki da ke gaban zababben shugaban kasar, a bangaren inganta yanayi na tattalin arzikin kasar.
Burin John Mahama na farko dai, shi ne kawo sauyi mai amfani a fannin sarrafa cocoa da kasar ke matsayi na biyu a kansa a duniya.
A ranar bakwai ga watan gobe ne dai za a rantsar da John Mahama a Ghana.