Joe Biden ya yi kira ga Jamus da ta kara tallafa wa Ukraine

Shugaba Joe Biden na Amurka ya bukaci Jamus ta ci gaba da goyon bayan UKraine domin ta samu nasara a yakin da take da Rasha tun bayan da ta mamaye ta fiye da shekaru biyun da suka gabata. A yayin ziyarar bankwana da ya kawo binin Berlin, Joe Biden ya ce kasar Ukraine na fama da hare-haren bama-bamai daga makaman Rasha sakamakon rashin samun asasshen taimako daga kasashen Yamma. Dama dai Jamus da ke zama kasa ta biyu wajen samar da makamai ga kyv bayan Amurka, ta rage yawan kudin taimako da ta ware wa Ukraine a shekarar 2025.

Karin bayani: Shugaba Joe Biden ya janye daga takara

Shugaba Joe Biden na Amurka na ganawa da shugabannin kasashen Turai ciki har da mai masaukin baki Olaf Scholz na Jamus da shugaban Faransa Emmanuel Macron domin mayar da hankali kan yakin da ake yi a Ukraine da kuma yankin Gabas ta Tsakiya bayan da Isra'ila ta yi ikirarin kashe shugaban Hamas Yahya Sinwar.

Karin bayani: Me goyon bayan Israila ke nufi ga Amurka?

Ziyarar ta Biden ta zo ne watanni uku kacal kafin karshen wa’adinsa na mulki. Saboda haka ne shugaban tarayar Jamus Frank-Walter Steinmeier ya tarbi shugaba Biden a fadarsa ta Bellevue da ke birnin Berlin don karrama shi da lamba mafi girma da Jamus ke bayarwasaboda ayyukan da ya yi wa al'ummarsa.


News Source:   DW (dw.com)