Joe Biden ya kammala ziyara a yankin Gabas Ta Tsakiya

Joe Biden ya kammala ziyara a yankin Gabas Ta Tsakiya
Shugaban kasar Amirka Joe Biden ya kammala ziyarar aiki da ya kai yankin Gabas ta Tsakiya a koron farko tun bayan darewa madafun iko watanni 18 da suka gabata

Ziyarar da ya karkare da halartar taron koli na majalisar kawancen hadin kai na kasashen yankin Gulf mai mambobin shidda da kuma kasashen Masar da Jordan da Iran da suka hallarci taron, Biden ya jaddada matsayar Amirka na ci gaba da zama babbar kawa ga  kasashen yanki.

Mahukunta a Isra'ila na fatan wannan ganawa da shugaba Biden ya yi da shugabannin kasashen ya taimaka wajen samar da kungiyar  kawancen tsaro da ita ma za a saka ta a ciki, a wani mataki na kara hadin kai domin tunkarar barazanar da kasar Iran ke da shi ga yankin.

A ganawar da ya yi da yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman, Joe Biden ya tabo batun mutunta 'yancin dan adam, da batun tsagaita wuta a kasar Yemen gami da batun kisan dan jaridar nan Jamal Khashoggi.


News Source:   DW (dw.com)