Sakamakon wucin gadi na babban zaben kasar Angola da aka gudanar a ranar laraba ya nunar da cewa jam'iyyar MPLA mai mulki na kan gaba da yawan kuri'u. Hukumar zabe ta kasar ta ce ya zuwa yanzu kashi 33% na kuri'u ne aka kirga, amma MPLA ta samu kashi 60.6% na kuri'un da aka tantance. Ita kuwa jam'iyyar adawa ta UNITA karkashin jagorancin Adalberto Costa Junior ta samu 33.8% na kuri'un da aka kada.
Shugaba Joao Lourenco na MPLA da ya dare kan karagamar mulki a 2017 na neman wa'adi na biyu duk da komabayan arziki da Angola ke fama da shi. Galibin matasan kasar dai na fama da zaman kashe wando duk da kasancewar Angola a matsayin kasa ta biyu mafi arzikin man fetur a Afirka.
Tun lokacin da Angola ta samu 'yancin kai daga Portugal ne jam'iyyar MPLA ke mulkin kasar. Sai dai manazarta na ganin cewa UNITA na da damar yin nasara a bana, saboda kuncin rayuwa da al'umma ke fuskanta.