Rahotannin da ke fitowa daga jihar Sokoto a Najeriya, na cewa wani hadarin jirgin ruwa, ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutum 29 a yankin karamar hukumar Shagari.
Kwale-kwalen wanda ke dauke da mutane 35 ya nitse ne a kogin Shagari, kuma gwanayen ninkaya sun ceto wasu mutum shida a cewar Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto.
Daga cikin wadanda suka mutun dai har da wasu kananan yara biyar.
Shaidu sun ce galibin wadanda ke cikin kwale-kwalen mata ne, kuma ya zuwa yanzu ba a sanar da musabbabin hadarin ba.
Sai dai ana danganta irin wadannan haduran da daukar mutane da ma kaya fiye da kima, sai kuma rashin matakan ceto fasinja a lokutan ibtila'i.