Jirgin fasinja ya yi karo da na soji a Amurka

Wani jirgi dauke da fasinjoji 60 da kuma ma'aikata hudu ya yi karo da jirgi mai saukar ungula na sojoji a kusa da birnin Washington na Amurka.

Jiragen sun yi karo ne a yayin da na fasinjojin ke kokarin sauka a filin jirgin Ronald Reagan lamarin da ya tilasta fara aikin gaggawa na ceto mutane a kogin Potomac.

Ya zuwa yanzu an gano gawarwaki 18 daga cikin kogin kuma masu aikin ceto na can na ci gaba da lalube ko za su dace.

Karin bayani da hukumomi suka bayar kamar yadda kafafen yada labaran Amurka suka ruwaito shi ne jirgin sojin da aka yi karo da shi  ya na atisaye ne a yankin.

Mutane 20 sun mutu bayan faduwar jirgi a Sudan ta Kudu

Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Amurka ta ce hadarin ya faru ne da karfe tara na dare agogon kasar a daya daga cikin wurare da ke da tabbacin tsaron sararin samaniya a duniya.

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce an sanar da shi dukkan halin da ake ciki kan hadarin da ake ci gaba da neman fasinjojinsa.

Trump ya yi wa wadanda suka rasu sakamakon hadarin addu'ar samun rahamar ubangiji tare da bai wa iyalansu hakurin jure 'yan'uwansu da suka rasa.

Mutane 179 sun mutu a hadarin jirgi a Koriya ta Kudu

Masu bincike na kokarin tattara bayanai ciki har da abinda ya faru a lokutan karshe na karon jiragen da kuma yadda aka yi jirgin fasinjojin ya baude wa hanyarsa.

Rahotanni sun nuna cewa jirgin mai lamba 5342 da ya shirya sauka a filin jirgin Regan na gudun mil 140 ne kan ko wace sa'a a lokacin da ya rasa hanyarsa a kan kogin Potomac.

Ya zuwa yanzu an gano gawarwaki 18 daga cikin kogin kuma masu aikin ceto na can na ci gaba da lalube don gano karin gawarwaki.


News Source:   DW (dw.com)