Shekaru 11 bayan girgizar kasa ta tsunami da ibta'ilin fashewar cibiyar makamashin nukiliyar Fukushima a Japan, firaministan kasar Fumio Kishida, ya ce kasarsa na duba yiwuwar gina wasu sabbin cibiyoyin nukiliya. Kishida ya fadi haka ne a Larabar nan a yayin wani taro kan makomar kasar. Ya ce ''dangane da batun cibiyoyin nukiliya, baya ga tabbatar da farfado da akalla 10 daga cikinsu, za mu duba yiwuwar farfado da sauran cibiyoyin da suka daina aiki a sassan kasar nan.''
Kasar ta Japan dai na da cibiyoyin nukiliya 33 da ta gina da zummar samar ma kanta da makamashin lantarki. Sai dai kawo watan da ya gabata, guda bakwai ne kawai ke aiki.
Rikicin Rasha da Ukraine wanda ya sabbaba karancin makamashi a duniya ne ya sanya Japan wacce fashewar cibiyar nukiliyar Fukushima ta haddasa wa gagarumar asara, sake tunanin farfado da cibiyoyin nukiliyar. A karshen shekarar ne dai mahukuntan na Tokyo za su yanke matsaya ta karshe a kan yunkurin nasu.