Japan za ta bai wa Afirka tallafin dala biliyan 30

Japan za ta bai wa Afirka tallafin dala biliyan 30
Japan ta ware kimanin dala biliyan 30 a matsayin tallafi ga kasashen Afirka da suka fuskanci koma baya a sakamakon annobar corona da yakin Rasha da Ukraine.

Shugabanin kasashen Afirka da Japan da kungiyoyin kasa da kasa sun fara taron shekara na habaka kawancen ci-gaban Afirka. Taron na gudana ne a birnin Tunis na kasar Tunisiya. Matsaloli na tsaro da ta'asar annobar corona da ma yakin Rasha da Ukraine na daga cikin batutuwan da mahalarta taron za su tattauna da zummar samar da mafita.

Gwannatin Japan ce ta kirkiri taron da aka yi wa lakabi da TICAD a shekarar 1993 kafin ya zama na hadin gwiwa bayan da Majalisar Dinkin Duniya da babban bankin duniya dama Kungiyar tarayyar Afirka suka hada kai, wajen lalubo hanyoyin da za a ciyar da nahiyar Afirka gaba da kuma magance matsalolin da suka hana mata ruwa gudu. Tuni Japan ta yi alkawarin tallafa wa Tunisiya da dala miliyan dari don rage radadin annobar corona ga tattalin arzikin kasar. Shugaban Japan Fumio Kishida bai samu damar halartar taron ba a sakamakon kamuwa da cutar corona da ya yi.
 


News Source:   DW (dw.com)