Japan na tunawa da harin Hiroshima

Japan na tunawa da harin Hiroshima
A wannan Asabar din ce Kasar Japan ke tunawa da zagayowar ranar da Amirka ta harba makamin kare dangi a Hiroshima shekaru 77 da suka wuce a lokacin yakin duniya na biyu.

A taron na bana, sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bi sahun dubban mutane da suka yi dandanzo a tsakiyar birnin don nuna alhini ga iftila'in da ya yi sanadiyar mutuwar mutane kimanin dubu 140 kafin karshen shekarar 1945. Wannan dai shi ne karo na biyu da sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya taba halatar wannan taron.

Daga cikin wadanda suka halarci taron har da Firanministan Japan Fumio Kashida wanda dan asalin Hiroshiman ne. Kashida wanda ya zabi birnin a matsayin inda za a gudanar da taron koli na kasashen G7 a badi, ya yi kira ga duniya da ta yi watsi da makaman Nukiliya.

Amirka ta soma jefa makamin Nukiliya na kare dangi a birnin Hiroshima kafin ta jefa na biyun a Nagasaki, lamarin da ya sa Japan mika wuya a yayin yakin duniya na biyu.
 


News Source:   DW (dw.com)