Japan: Murabus din shugaban 'yan sanda

Japan: Murabus din shugaban 'yan sanda
Shugaban hukumar 'yan sandan kasar Japan, Itaru Nakamura ya sanar da cewa zai yi murabus, saboda gaza kare firaministan kasar Shinzo Abe da wani ya bindige shi har lahira.

Nakamura dai shi ne jami'in dan sanda mafi girman mukami a Japan na farko da ya sauka daga mukaminsa, tun bayan afkuwar kisan gillar na Abe da ya girgiza kasar. Yayin wani taron manema labarai da ya gudanar, Nakamura ya bayyana sakamakon bincike kan kisan na Abe da ya nuna cewa an gaza ba shi kariya daga bayansa saboda rashin yin tunanin yiwuwar kai masa hari. Da ma tuni Nakamura ya bayyaana nadama kan gazawar 'yan sanda wajen bai wa Abe kariya, yayin gangamin yakin nemana zaben da aka harbe shi har lahira a wajen.


News Source:   DW (dw.com)