Janye dakarun Faransa daga Chadi

Shugaba Mahamat Idriss Deby na kasar Chadi ya yi maraba da matakin janye dakarun Faransa daga kasarsa, abin da ya kawo karshen zaman dakarun a kasar da ke yankin tsakiyar nahiyar Afirka. Bayan ganawa da dakarun da suka fice a sirrance, daga bisani shugaban ya gabatar da jawabi ga dakarun kasarsa gami da jami'an diflomasiyya a birnin N'Djamena fadar gwamnatin kasar.

Karin Bayani: Faransa ta hannata wa Chadi sasanin sojinta na karshe a yankin Sahel

Dakarun Faransa a ChadiDakarun Faransa a ChadiHoto: Aurelie Bazzara-Kibangula/AFP/Getty Images

Dakarun na Faransa sun mika sansaninsu ga dakarun kasar ta Chadi. Shugaba Mahamat Idriss Deby  ya tabbatar da cewa kasarsa ta Chadi za ta ci gaba da dangantaka da Faransa bayan janye dakarun kuma dangatakar za ta kara inganta. Galibin kasashen Afirka da Faransa ta yi wa mulkin mallaka sun bukaci ta janye dakarunta, inda yanzu haka ake tattaunawa kan janye dakarun na Faransa daga kasar Senegal zuwa karshen wannan shekara ta 2025 da muke ciki.

 


News Source:   DW (dw.com)