Jamusawa na ci gaba da zuwa rumfunan zabe don kada kuri'a

Jamusawa na ci gaba da tururuwar zuwa rumfunan zabe don kada kuri'a a babban zaben kasar na Lahadi, wanda ake hasashen 'dan takarar hadakar jam'iyyun CSU/CDU Friedrich Merz ne zai samu nasarar kafa gwamnati.

Merz wanda shi ne jagoran jam'iyyar CDU, ya jefa kuri'arsa a garinsa na Hochsauerland bisa rakiyar matarsa Charlotte Merz, sannan ya tafi ba tare da gabatar da wani jawabi ga 'yan jarida ba, amma ya dagawa jama'a hannu.

Karin bayani:Jamusawa na zaben sabuwar gwamnati a Lahadin nan

Haka zalika shi ma 'dan takarar jam'iyyar SPD shugaban gwamnatin Jamus mai barin gado Olaf Scholz ya kada tasa kuri'ar a garin Potsdam da ke kusa da birnin Berlin, bisa rakiyar mai dakinsa Britta Ernst.

Zaben na zuwa ne watanni bakwai kafin ainihin lokacinsa, sakamakon rushewar gwamnatin hadaka karkashin jagorancin Olaf Scholz a cikin watan Nuwamban bara, bayan fama da rikicin cikin gida.

 


News Source:   DW (dw.com)