Jamusawa ba su gamsu da Scholz ba

Jamusawa ba su gamsu da Scholz ba
Bincken ya nuna kaso 65 cikin 100 na Jamusawa na da ra'ayin shugaban gwamnati ba ya aikinsa yadda ya kamata, duk da kwarewar da ya samu a tsohuwar gwamnatin Angela Merkel.

Kusan kaso biyu cikin uku na mutanen Jamus sun nuna rashin gamsuwa da kamun ludayin shugaban gwamnati Olaf Scholz da gwamnatinsa ta hadaka. Wannan ya biyo bayan rikice-rikice dabam-dabam da suke ta bijiro wa gwamnatin ta Scholz wacce ta fara aiki a watan Disambar da ya gabata.

Wani binciken jin ra'ayin jama'a da aka wallafa a jaridar Jamus ta Bild am Sonntag ya ce kaso 25 cikin 100 na Jamusawa ne kawai ke farin ciki da gwamnatin hadakar da jam'iyyar SPD ke jagoranta.

Tun bayan da ya karbi iko da kasar mafi karfin arziki a nahiyar Turai, Olaf Scholz, ya fuskanci kalubalen rikicin Ukraine da takaddamar cinikin makamashi da Rasha, ga kuma tsadar rayuwar da yanzu ke barazanar jefa tattalin arzikin Jamus cikin mawuyacin hali.


News Source:   DW (dw.com)