Jamus za ta halasta shan tabar wiwi

Jamus za ta halasta shan tabar wiwi
Jamus ta bi sahun sauran kasashen Turai a son aiwatar da dokar halasta siya da shan tabar wiwi ga masu bukatar sha don nishadi a bainar jama'a.

A wannan Talatar, kwararru a Jamus za su soma nazarin aiwatar da dokar halasta siya da shan tabar wiwi ga masu bukatar shanta don nishadi a bainar jama'a. Ma'aikatar Lafiya ta kasar, ta shirya gudanar da taron da zai hada kan wakilai daga sassa dabam-dabam da kuma kwararru daga fannin lafiya da shari'a dama sauransu, da za su yi nazari kan batun a zaman da aka shirya yi a birnin Berlin .

Wannan dama na daya daga cikin alkawuran da jam'iyyun da suka shiga hadaka da jam'iyyar SPD ta Shugaban gwamnatin Olaf Scholz suka cimma a bara, inda aka amince da a bai wa rukunin da suka mallaki takardar lasisi izinin sayar da tabar da kuma bai wa wadanda shekarunsu ya kai damar mu'amala da wiwin don nishadi a bainar jama'a. 


News Source:   DW (dw.com)