Gwamnatin Jamus ta yi alkawarin gudanar da bincike domin fayyace kurakuren da hukumomin kasar suka yi na gaza yin rigakafin harin da aka kai kasuwar Kirisimeti ta birnin Magdeburg a ranar Juma'a.
Masu binciken za su saurari bahasi daga ministar cikin gida Nancy Faeser a ranar 30 ga wannan wata na Disamba kan rashin yin katabus daga jami'an tsaro na dakile aukuwar wannan lamari.
Karin bayani: Ana bincike kan barazanar sake kai hari a Jamus
Mujallar Der Spiegel ta ruwaito cewa, shekara guda da ta gabata hukumomin leken asirin Saudiyya sun aike wa takwarorinsu na Jamus gargadi a game da dabi'un maharin, sai dai ba a dauki wani mataki a kansa ba.
Wannan lamari ya birkita lissafi a Jamus tare da janyo matsin lamba ga gwamnatin Olaf Scholz, yayin da ya rage watannin biyu a gudanar da zaben gaba da wa'adi na 'yan majalisun dokoki ta Bundestag.