Jamus za ta bai wa Lebanon tallafin Euro miliyan 60

Jamus za ta tallafa wa Lebanon da kudi Euro miliyan 60 kwatankwacin kusan dala miliyan 65, don farfado da ita daga rushewar da take fuskanta sanadiyyar yakin Isra'ila da Hezbullah, wanda ya janyo rincabewar rikicin yankin Gabas ta Tsakiya.

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ne ya sanar da hakan ga firaministan Lebanon Najib Mikati ta wayar tarho a daren Laraba, kamar yadda kakakin fadar gwamnatin Jamus Steffen Hebestreit ya tabbatar.

Mr Scholz ya nanata kudurin ggwamnatinsa na sake agaza wa Lebanon, a taron kaddamar da gidauniyar taimakonta da za gudanar a Alhamis din nan a birnin Paris na kasar Faransa, wanda shugaba Emmanuel Macron ya shirya, inda tuni ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock ta kama hanyar zuwa taron.

Karin bayani:Yaki ka iya mamaye Gabas ta Tsakiya - Scholz

Sauran mahalarta taron sun hada da wakilai daga Majalisar Dinkin Duniya da na kungiyar tarayyar Turai EU, da sauran kungiyoyin bayar da agaji na duniya.

A Alhamis din nan ce shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz zai kai ziyarar aiki ta wuni uku kasar Indiya, don gana wa da firaministan kasar Narendra Modi, a wani mataki na kara karfafa dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.

karin bayani:Kamfanin Lufthansa da abokan huldarsa sun soke jigila zuwa Isra'ila

Daga cikin muhimman batutuwan da shugabannin biyu za su tattauna akwai al'amuran tsaro, musamman yadda za a kawo karshen yakin Rasha da Ukraine, kasancewar Indiya na da kyakkyawar alaka da Rasha da kuma kasashen yamma, sai sha'anin tattalin arziki, har da illolin da matsalar dumamar yanayi ke haddasa wa, da kuma batun bai wa Indiyawa damar zuwa Jamus don yin aiki.

A yayin ziyarar ta sa, Mr Scholz zai samu rakiyar ministan sha'anin tattalin arziki Robert Habeck da na kwadago Wolfgang-Hubertus Heil da kuma na tsaro Boris Pistorius, yayin da ministar harkokin wajen kasar Annalena Baerbock za ta same a can daga bisani, bayan halartar taron Faransa.

 


News Source:   DW (dw.com)