Jamus za ta bai wa Kiev makamai masu yawa

Jamus za ta bai wa Kiev makamai masu yawa
Jamus ta shirya tura makamai da kudinsu ya kai Euro miliyan 500 zuwa Ukraine, domin taimaka wa kasar a yakinta da Rasha, a cewar kakakin shugaban gwamnati Olaf Scholz.

Kiev na shirin karbar makamai da suka hadar na kare kanta da motoci yaki masu sulke da wasu muhimman kayan fada a cewar sanarwar da aka gabatar a wannan Talata, a dai dai lokacin da kansilan ke ziyara a Canada.

Ba da jimawa ba ne dai Scholz ya yi alkawarin karin gagarumin taimakon kudi da tallafin soji wa Ukraine. Tun a farkon wannan shekarar ce dai Jamus din ta yi ta kokonto kan ko ya dace ta taimakawa Ukraine da makamai, batun da ya haifar da jinkiri mai tsawo da kuma kace-ka na ce a cikin gida da waje.

 


News Source:   DW (dw.com)