Fadar gwamnati da ke birnin Berlin, ta ce kasar ta Jamus na kokarin daukar matakai ne cikin hanzari ne domin bai wa musamman Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da cutar ke ta'adi a cikinta tallafin na rigakafin cutar Kyandar Biri.
Haka zalika, mai magana da yawun gwamnatin Jamus ya sanar da cewa gwamnatin za ta bai wa Hukumar Lafiya ta Duniya WHO kudade domin taimaka wa aikin yaki da cutar ta Kyandar Biri.
A farkon wannan watan ne dai Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cutar a matsayin matsalar lafiya da ke bukatar mataki na gaggawa a duniya a yanzu.
Haka nan ma an samu wasu da suka kamu da cutara kasashen yankin Asiya da ma nahiyar Turai.