Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya jaddada matsayar gwamnatinsa na hana Rasha cimma burinta na mamaye Ukraine, Scholz ya ce wajibi Berlin ta kara wa Ukraine makamai don kare kanta daga barazanar dakarun Moscow.
Olaf Scholz ya gayawa majalisar dokokin Jamus ta Bundestarg cewa, gwamnati na tattaunawar sirri da hukumomin Kyiv game da yiwuwar tabbatar da tsaro ga barazar da Moscow ke yi wa Ukraine
Gwamnatin Ukraine ta nemi agajin tsaro daga kasashen Turkiyya da China da Jamus, bayan da Rasha ta hanata zama mamba a kungiyar hadakar tsaro ta NATO.
News Source: DW (dw.com)