Jamus: Yiwuwar samun farmakin kyama

Jamus: Yiwuwar samun farmakin kyama
Shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier ya yi gargadin sabuwar barazana daga masu tsattsauran ra'ayin kyamar baki, a daidai lokacin da ake bikin cika shekaru 30 bayan kai harin wariyar launin fata mafi muni a kasar.

Shugaban kasar ta Jamus Frank-Walter Steinmeier ya bayyana hakan ne a birnin Rostock da ke arewacin kasar, yayin tunawa da harin wariyar launin fatar da ya afku a shekara ta 1992 yayin da wasu dubban mutane suka rika kuwwa da tafi ga wani mahari da ya farmaki gidan ajiye masu neman mafaka. Ya kara da cewa Jamus ta gaza kawo karshen kiyayya da tsattsauran ra'ayin kyamar baki tsawon shekaru, a daidai lokacin da 'yan siyasa ke gargadin yiwuwar samun 'yan tawaye a lokacin sanyin hunturu a bana sakamakon tsadar makamashi da hauhawar farashi da kuma matakan yaki da annobar corona.

 


News Source:   DW (dw.com)