Dan bindigar mai shekaru 21 da haihuwa, ya bude wuta a wata makarantar sakandare da ke arewacin Jamus, inda ya yi wa wata mata mummunan rauni kafin ya shiga hannun 'yan sanda. A wani lamari na dabam 'yan sanda a birnin Leipzig da ke gabashin Jamus din sun tsare wani dan makarantar sakandare mai shekara 21, bayan da ya wallafa hotunansa da bindiga a shafin Snapchat tare da yin barazana. Sai dai 'yan sandan sun ce bincike ya gano bindigar ta roba ce, kuma bidiyon da ya wallafa wani bangare ne na aikin makaranta.
A makon da ya gabata, masu bincike a birnin Essen sun dakile harin bam a makaranta, bayan sun kama wani matashi dan shekaru 16 da ake zargin yana shirin kai harin ta'addanci na 'yan Nazi. A watan Janairun 2022, wani dalibi dan shekara 18 ya bude wuta a wani dakin karatu na jami'ar Heidelberg da ke Kudu maso yammacin Jamus, inda ya kashe wata budurwa tare da raunata wasu mutane uku.
A shekara ta 2009 ma wani tsohon dalibin wata makaranta, ya kashe dalibai tara da malamai uku a Winnenden da ke jihar Baden-Wuerttemberg ta Jamus. Daga bisani dai, dan bindigar ya kashe kansa. A shekara ta 2002, wani tsohon dalibi dan shekara 19 ya harbe mutane 16 a wata makaranta da ke birnin Erfurt a tsakiyar Jamus, kafin shi ma ya kashe kansa daga bisani. Wadannan hare-hare dai sun sa gwamnatin Jamus tsaurara dokokin mallakar bindiga, inda aka bukaci tilasta 'yan kasa da shekaru 25 su yi gwajin lafiyar kwakwalwa kamin neman lasisin mallakar bindiga.