Firaministan Burtaniya Keir Stammer da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron su ma sun baiyana makamancin wadannan kalamai na sukar lamirin Elon Musk kan yin katsalandan a siyasar wata kasa.
Firaministan Norway Jonas Gahr Stoere ya baiyana damuwa cewa dan kasuwar na neman jefa kansa cikin siyasar wata kasa da ba ta Amurka ba, yana mai cewa ba haka dimukuradiyya ta ke ba.
Musk wanda babban na hannun daman zababben shugaban Amurka Donald Trump ne a watan da ya gabata ya nuna goyon bayansa ga jam'iyyar AfD mai akidar kyamar baki a Jamus. Wannan dai na zuwa ne gabanin zaben da za gudanar a kasar a watan Fabrairu mai zuwa. Haka ma kuma ya yi irin wannan kalaman a kan siyasar Burtaniya.