Ziyarar ta Baerbock a yankin dai na da nasaba ne da kokarini da ake yi na ganin an cimma tsagaita wuta a yakin Isra'ila da kungiyar Hamas a Zirin Gaza.
Babbar bukatar ita ce ta ganin an sako 'yan Isra'ila da ke hannun kungiyar Hamas da kuma kara agajin jinkai a Zirin Gaza da yaki ya daidaita.
Gabanin isar babbar jami'ar diflomasiyyar Jamus din a birnin Tel Aviv, Baerbock ta ziyarci kasashen Saudiyya da kuma Jordan.
Watanni 11 da fara yaki a tsakanin Isra'ila da Hamas, cikin wannan makon gwamnatin Amurka ta ce akwai alamun samun nasarar cimma tsagaita wuta da ake buri.