Jamus ta rage hasashe bunkasa

Jamus ta rage hasashe bunkasa
Kasar Jamus mafi karfin tattalin arziki tsakanin kasashen Turai ta rage hasashen bunkasa da kasar za ta samu cikin wannan shekara ta 2022.

Kasar Jamus ta rage yawan girman bunkasa tattalin arzikin da kasar take tsinkaye cikin wannan shekara ta 2022, sakamakon kutsen da Rasha ta kaddamar a kan Ukraine.

Ma'aikatar kula da tattalin arzikin kasar mafi girman tattalin arzikin tsakanin kasashen Turai ta nuna yuwuwar samun bunkasan tattalin arziki na kashi 2.2 cikin 100, maimakon kashi 3.6 cikin 100 da kasar ta yi hasashe a farkon shekara gabanin barkewar yaki a Ukraine.

Robert Habeck ministan kula da tattalin arzikin kasar ta Jamus ya kuma kara da cewa Jamusawa za su fuskanci tashin farashin kayayyaki fiye da kowane lokaci cikin shekaru da dama sakamakon yanayin da duniya ta samu kanta a ciki.

 


News Source:   DW (dw.com)