Jamus ta nuna damuwa da kalaman Abbas

Jamus ta nuna damuwa da kalaman Abbas
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya baiyana damuwa da kalaman shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas kan kisan kiyashi da aka yiwa Yahudawa.

A wannan laraba gwamnatin ta gayyaci babban jami'i diflomasiyya a ofsihin jakadancin Falasdinawa dake Berlin domin nuna rashin jin dadi da yadda shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas ya kwatanta matakan Israila da kisan kare dangi.

Kakakin gwamnatin Jamus yace a baiyane yake ga gwamnatin Jamus da shugabanta cewa azabtarwa da kisan gillar da aka yi wa Yahudawa miliyan shida a Turai mummunan laifi ne na cin zarafin dan Adam wanda ba zai misaltu ba ballanta a yi kwatance da shi.

A yayin ziyarar da ya kawo Berlin a ranar talata shugaban na Falasdinawa ya zargi Israila da aikata kisan kare dangi har sau hamsin yayin da yake maida martani ga wata tambaya da aka yi masa game da bikin cika shekaru 50 na harin da wasu tsaregun Falasdinawa suka aka kai wa tawagar Israila yayin gasar Olympics a birnin Munich a shekarar 1972.
 


News Source:   DW (dw.com)