Jamus ta kori malamin 'yan shi'a daga kasar

Umurnin da ma'aikatar cikin gida ta jihar Hamburg ta bai wa Mofatteh na bukatar malamin dan kasar Iran ya bar Jamus cikin kwanaki 14 ko kuma hukumomin Jamus su yi amfani da karfi su mayar da shi kasarsa. Bisa dokokin Jamus, idan har da malamin zai ki mutunta umurnin, zai iya fuskantar hukuncin dauri na shekaru uku a gidan yari.

Jami'an leken asirin Jamus ne suka bukaci arufe cibiyarda malamin ke jagoranta bisa zargin kasar Iran da kokarin cimma wasu manufofi ta hanyar amfani da cibiyar da ke nan Jamus. Ministar harkokin cikin gida Nancy Faeser ta ce malamin ya yi amfani da cibiyar wajen tallata tsauraran akidua Jamus.


News Source:   DW (dw.com)