Jamus ta kaddamar da shafin intanet na samun biza cikin sauki

Ma'aikatar harkokin wajen Jamus ta kaddamar da wani shafi a yanar gizo na neman takardun izinin shiga kasar wato biza, tsarin da a cikin wata sanarwa ministar harkokin waje Annalena Baerbock ta bayyana shi a matsayin gagarumin ci-gaba da aka dade ana jira.

Sanarwar ta ce an samar da shafin ne da nufin kawo sauki ga masu neman takardun izinin aiki ko karatu a Jamus da kuma bai wa masu aiki a kasar damar kawo iyalensu kusa da su cikin sauki.

Karin bayani: Matsalar samun bizar Jamus ga 'yan Afirka

Baerbock ta kuma kara da cewa tsarin zai rage wa Jamus asarar guraben aiki kusan 400,000 da take yi saboda wahalhalu samun takardun izinin zuwa kasar wato biza.

Shafin ya fara aiki tun daga ranar daya ga wata Janairu na wannan sabuwar shekara ta 2025 kuma yana ba da damar shiga ofisoshi 167 da ke bayar da bizar Jamus a sassa dabam-dabam na duniya.


News Source:   DW (dw.com)