Jamus ta amince da ta kara yawan dakarun wanzar da zaman lafiya da ta tsugunar a Mali. An kara yawan sojojin zuwa dubu daya da dari hudu daga dubu daya da dari daya, shiri ne na son ganin an cike gibin da janyewar sojojin Faransa daga cikin kasar ya haifar. Karin sojojin dari uku za su hade da sojojin nan na kasa da kasa na MINUSMA.
Rundunar sojin Jamus ta Bundeswehr a Malin na da muradin ganin kasar Mali da ta sha fama da rikicin mulki a sakamakon juye-juyen mulki baya ga aiyukan 'yan ta'adda da suka addabi yankin Sahel, ta tsaya da kafafunta tare da komawa kan tafarkin mulkin dimukradiyya.