Jamus ta bukaci bayanai daga jami'in diflomasiyyar Koriya ta Arewa sakamakon karuwar damuwa na goyon bayan da Pyongyang ke bai wa Rasha a yakin da ta ke yi a Ukraine.
Idan har ta tabbata sojojin Koriya ta arewa suna cikin Ukraine kuma Koriya ta arewa na taimaka wa Rasha da sojoji a yakin, to hakan zai zama babban keta dokokin kasa da kasa kamar yadda ma'ikatar harkokin wajen Jamus ta wallafa a shafin sada zumunta na X
Taimakon da Koriya ta Arewa ke bai wa Rasha na barazana kai tsaye ga tsaron Jamus da kudirin zaman lafiya na tarayyar Turai.